A ranar 1 ga watan Disamba, an yi taron shekara-shekara na kwalejojin Confucius da jami’ar BFSU ta dauki nauyin koyarwa kuma taron tattaunawar masanan gida da waje na kwalejojin Confucius a BFSU. Wannan taro shi ne taro na karo 12 da BFSU ta shirya, kuma taken taro shi ne “Salon koyarwa da ingancin koyarwa na kwalejojin confucius”. Mambobi da shugabanni 44 da suka fito daga gida da waje na kwalejojin Confucius na BFSU sun halarci taron.