A ranar 4 zuwa ranar 5 ga watan Disamba, an yi taron kwalejin Confucius karo na 13 a birnin Chengdu. Mataimakiyar firaministan kasar Sin kuma shugabar kwamitin cibiyar kwalejin Confucius ta Sin Madam Sun Chunlan ta halarci bikin bude taro, tare da yin jawabin fatan alheri. Taken taron shi ne “Gyare-gyare da kirkiro sa sabbin tunani don samun bunkasuwa da samu makoma mai haske kafada da kafada”, inda aka yi tarurrukan tattaunawa guda 2, da tarurrukan tattaunawa tsakanin shugabannin jami’o’in gida da waje 8 da tarurrukan nazari guda 20. Wakilai sama da 1500 da suka fito daga kasashe da yankunan 154 sun halarci taron. Shugaban BFSU Peng Long da mataimakinsa Yan Guohua sun halarci taron. Ministan ilmi na Sin kuma mataimakin shugaban kwamitin cibiyar kwalejin Confucius na Sin Chen Baosheng ya shugabanci taron.
BFSU ta sami lambar kyauta ta fitacciyar hukumar hadin gwiwa ta kwalejin Confucius, mataimakin ministan Sin Tian Xuejun ya mika lambar yabo ga Yan Guohua. Kwalejojin Confucius na Barcelona da na Rome da na Nuremberg – Erlangen sun sami lambar yabo ta kyawawan kwalejin Confucius a duniya.