
A ranar 5 ga watan Yuni, an kaddamar da bikin bude kwas na kasa da kasa na lokacin hutu na zafi na shekarar 2021 a jami’ar BFSU.
Kwararrun kasashen daban daban sun gabatar da kansu ta hoton bidiyo. A bana, an gayyaci kwararrun kasashen duniya 13 don su ba da lecca a lokacin hutu, inda za su koyar da fannonin harsuna, siyasa, zamantakewar al’umma, tattalin arziki, tarihi, dangantakar kasa da kasa, shirin raya shiyya-shiyya, yada labaru, adabi da fasaha da sauransu, daliban gida da waje 181 sun halarci kwas.