A ranar 29 ga watan Afrilu, aka ƙaddamar da bikin raya gamayyar nazarin ƙasashen duniya da shiyya-shiyya da fannonin karatu CCAS a BFSU.
Ƙawacen jami’o’in harsunan wajen duniya GAFSU ya ɗauki nauyin kafa wannan gamayya, wanda ke ƙunshe da masana daga ƙasashe 181, waɗanda suka yi nazari kan harsuna sama da 100. Bisa ra’ayin ƙara fahimtar duniya da ƙago makoma mai haske, an kafa wannan dandalin masanan duniya.
Shugaban BFSU, shugaban gamayyar Yang Dan ya yi jawabin fatan alheri, inda ya gabatar da ra’ayinsa game da fannoni uku wajen kafa wannan ƙawacen nazari a duniya. Na farko, ya kamata a magance ƙalubalen duniya da more damar da aka samu, ta hakan za a ƙara haɗin gwiwa tsakanin masanan ƙasashen duniya da shiyya-shiyya. Na biyu, a ƙara haɗin gwiwa tsakanin masanan duniya da shiyya-shiyya, kamata ya yi a kawar da shingaye, da sa ƙaimi ga haɗin gwiwa, don haɗa mabambanta fannonin karatu tare da ƙirƙiro da sabbabin nazari. Na uku, ya kamata a mayar da hankali kan ƙasashen duniya da suka shiga ciki, musamman ma gudummawar da ƙasashe masu tasowa suka bayar.
Tsohon direktar hukumar kula da ilmi da kimiyya da al’adu na M.D.D. UNESCO Irina Bokova da shugaban BFSU Li Yansong, da jami’in da ke kula da tsarin M.D.D. da ke ƙasar Sin Chang Qide, da shugaban kwalejin nazarin ƙasashen duniya da shiyya-shiyya na jami’ar Peking Qian Shengdan, da shugaban cibiyar nazarin siyasa na kwalejin nazarin kimiyya da zamantakewar al’umman Sin Zhang Shuhua da shugaban kwalejin nazarin kasar Sin na jami’ar Fudan Zhang Weiwei sun yi jawabi ɗaya bayan ɗaya.
Babban sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua da shugaban ƙawacen gamayyar kuma shugaban BFSU Yang Dan da shugaban haɗaɗɗen kwamintin nazarin Confucius da al’adu na duniya Roger T. Ames sun ƙaddamar da wannan ƙawacen CCAS tare, A yayin bikin, an gabatar da alamar ƙawacen da burinsa.
Bayan da aka kammala bikin, an ci gaba da taron tattaunawar nazarin ƙasashen duniya da shiyya-shiyya kan fannonin karatu.