Babban Shafi > Labaru > 正文

BFSU ta shirya taron tattaunawar gyare-gyare da raya sha’anin koyar da ilmin harsuna a ƙasar ta 2022

Updated: 2022-05-22

A ranar 13 ga wata, an ƙaddamar da taron tattaunar gyare-gyare da raya sha’anin koyar da ilmin harsuna a makarantun firamare da sakandare na ƙasar Sin ta shekarar 2022. Jami’ar BFSU ta shirya wannan taron, wanda ya samu goyon baya daga kwamintin ilmi na ƙasar Sin.

Zaunannen mamba kuma mataimakin sakataren majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na ƙasar Sin kuma mataimakin shugaban kwamintin sa ƙaimi ga samar da dimokuradiyya Zhu Yongxin, da direktan sashen kula da makarantun firamare da sakandare na ma’aikatar ilmin Sin Lv Yugang, da sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua sun yi jawabi bi da bi game da gyare-gyare da ƙirƙiro da sabbin tunani game da ilmin koyar da harsuna, da raya ilmin makarantun firamare da na sakandare, da ɗaukar nauyin wajen koyar da harsuna a makarantun firamare da sakandare.

Jami’in da ke kula da harkokin koyarwa na wuraren daban daban, da malamai, da shugabanni, da manazarta a fannin koyar da Turanci a makarantun firamare da sakandare, da mambobin ƙawacen horar da ɗalibai na ƙasa da ƙasa na BFSU sun yi tattaunawa game da gyare-gyare da raya malamai a makarantun firamare da sakandare a ƙarƙashin sabon yanayin da ake ciki.

A yayin taron, an bayar da rahoto game da nazarin harsuna na shekara-shekara da hanyoyin lalubo bakin zaren ilmin koyar da harsuna a ƙasar Sin.