
Daga ranar 27 zuwa ranar 28 ga watan Mayu, BFSU ta gudanar da taron tattaunawar haɗin gwiwa da samun bunƙasuwar shiyya-shiyya na ƙasashen Sin da Japan da Koriya ta kudu na shekarar 2022 a shafin Intanet. Taken taron shi ne raya haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu a ƙarƙashin yanayin dunƙulewar tattalin arzikin shiyya-shiyya. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Yang Dan ya halarci taron kuma ƙwararru da masana kimanin 60 da suka fito daga jami’o’in BFSU, da UIBE, da jami’o’in Shandong, da Fudan, da Nankai, da cibiyar nazarin tattalin arzikin a gewayen tekun Japan, da jami’ar Kyoto, da jami’ar Chonnam sun halarci wannan taro.
An gabatar da tarurruka guda 5 a yayin taron tattaunawa, waɗanda suka ƙunshi haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa don tabbatar da tsaro da yaƙi da bala’i tsakanin ƙasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu, da taron amincewar juna da haɗin gwiwar siyasa tsakanin ƙasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu, da dunƙulewar tattalin arzikin shiyya-shiyya na Sin da Japan da Koriya ta Kudu, inganta haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe uku da ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashe arewa masi gabashin Asiya a ƙarƙashin yanayin duniya, ƙwararru da masana na ƙasashen uku sun more nasarorin da suka samu da zurfafa tattaunawa a tsakaninsu.