Babban Shafi > Labaru > 正文

BFSU ta shirya taron tattaunawar ƙoli game da koyar da harsunan waje

Updated: 2022-07-20

A ranar 12 ga watan Yuli, an gudanar da taron tattaunawar ƙoli game da ƙa’idojin da aka bi da yadda aka koyar da harsunan waje a kan shafin Intanet. Kwalejin nazarin Turanci na BFSU da kamfanin kula da ɗab’in littattafan koyar da harsunan waje da nazarinsa sun shirya wannan taro tare. Zaunannen mamban kwamintin jam’iyyar kwaminis ta BFSU kuma mataimakin shugaban BFSU Sun Youzhong ya halarci taron.

Farfesa Diane Larsen-Freeman na jami’ar Michigen, da Farfesa Matthew E. Poehner na jami’ar Pennsylvania, da Farfesa Wen Qiufang daga BFSU, da Farfesa Wang Chuming daga jami’ar koyon harsunan waje ta Guangdong, da Farfesa Wang Qiang daga jami’ar koyar da malanta, da Farfesa Xu Jinfen daga jami’ar nazarin kimiyya da fasaha ta gabashin ƙasar Sin, da Farfesa Zhang Lian sun yi jawabi bi da bi, inda suka tattauna ƙa’idojin da za a bi wajen koyar da harsunan waje.