A ranar 1 ga watan Agusta, an fara bikin buɗe kwas na horaswa na lokacin hutu na zafi na kyakkyawan al’adun Rasha da harshen Sinanci a birnin Beijing. Mataimakiyar shugaban jami’ar koyon harsuna na birnin Moscow Innara Guseinova da mataimakin sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU kuma mataimakin shugaban jami’ar Jia Wenjian sun halarci bikin.
Cibiyar kula da haɗin gwiwa kan mu’amalar harsunan gida da waje ta ma’aikatar kula da ilmi ta shirya wannan bikin, kuma ofishin kula da kwalejin Confucius na BFSU da kamfanin kula da ɗab’in littattafan koyar da harsunan waje da nazari sun shirya wannan biki tare. Wannan biki ya kasance wani aikin da aka shirya ga masu sha’awar Sinanci na ƙasar Rasha. An kwashe kwanaki 8 ana yinsa. An haɗa da koyon Sinanci da al’adun Sin, kuma an shirya wasu ɗarussa da lecca game da al’adu gwargwadon iyawarsu. Ɗalibai 207 da suka fito daga makarantu 60 a birane 31 na Rasha sun halarci bikin.
A lokacin hutu na zafi na shekarar 2022, ofishin kula da kwalejin Confucius zai ci gaba da shirya ayyukan mu’amala 10, waɗanda za su ƙunshe Rasha, Vietnam, Malaysia, ƙasashen renon Faransa, da ƙasashen Larabawa. An hada da Sinanci da rubuce-rubucen Sin da al’adu da abincin ƙasar Sin. Ya zuwa yanzu, yawan ɗaliban da suka yi rajista ya kai sama da 1000, an riga an shirya bukukkuwa guda 5.