A ranar 23 ga wata, an gudanar da taron tattaunawar bunƙasuwar Tibet ta Sin ta 2023 a babban ɗakin taron Beijing. Taken taron shi ne “Sabon yanayi, sabuwar Tibet, da sabuwar tafiya: Sabon babin kiyaye hakkin ɗan Adam da samun bunƙasuwa mai inganci na Tibet”. Ofishin kula da yada labaru na majalisar gudanarwar Sin da gwamnatin Tibet mai cin gashin kanta suka shirya tare, kuma BFSU ta ɗauki sauyin shirya shi.
Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’a, da malaman ƙasashen waje sun halarci wannan taron tattaunawar. Jakadu da jami’an diflomasiyya na ƙasashe da yankuna 36, da shugabannin kafofin yada labaru, da ƙwararru da masana na jami’o’i da hukumomin nazari, da ɗaliban ƙasashe waje, da masu fasaha, da ƙwararru na kamfanonin waje, da sauran shahararrun ƙwararru, da jami’ai sun halarci taron.
A yayin taron, Yang Dan ya yi jawabi mai take “Samun wadata da ci gaba mai ingancin tattalin arziki a tudu”, inda ya yi taƙaitaccen bayani game da tarihin aikinsa a jihar Tibet, da bincike da ya yi game da nazarin tattalin arziki, ya gabatar da ci gaba da Tibet ya samu wajen raya tattalin arziki, kuma ya bayyana labarin ƙasa na musamman da tattalin arziki na Tibet, don ya bayar da shawarwari game da kimiyyar samun wadata a Tibet.
An kafa wannan taron tattaunawa a rukuni guda 5, kuma cibiyar nazarin shiyya-shiyya da ƙasashe na BFSU ta shirya wannan taron tattaunawa na samun wadata da ci gaba mai inganci na Tibet.