Kwanan baya, ma’aikatar ilmin ƙasar Sin ta fidda da takardar sunayen waɗanda suka samu lambobin yabo a fannin koyarwar ta shekarar 2022, inda BFSU ta samu uku daga cikinsu.
Salon BFSU wajen horar da ɗalibai masu digiri na farko na harsunan daban daban ya samu lambar yabo ta farko, yayin da salon horar da fitattun ɗalibai masu neman digiri na farko wajen ƙirƙiro da sabbin tunani a fannin Turanci a ƙarƙashin yanayin da ake ciki ta samu lambar yabo ta biyu, kana kafa tsarin horar da fitattun masu fasara da harsunan daban daban bisa dabarun raya yada labarun duniya bisa manyan tsare-tsare ya samu lambar yabo ta biyu a cikin duk ayyukan horar da ɗalibai masu neman digiri na biyu a ƙasar Sin.