Kwanan baya, mujallar M.D.D. UN Today ta fidda da wani bayani mai take “Reaffirming International Connections through Language”,inda aka bayar da intabiyu da aka yi da shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin BFSU Yang Dan.
A yayin intabiyu, shugaban Yang ya bayyana fasahohin da BFSU ta samu ta hanyar da koyar da harsuna da sa kaimi ga mu’mala tsakanin ƙasashen duniya, kuma ya bayyana nasarorin da BFSU ta samu wajen inganta haɗin gwiwa a wajen koyar da harsunan waje, kana ya amsa tambayoyin da aka bayar gare shi game da kalubale da damar da aka fuskanta a ƙarƙashin yanayin bunƙasuwar AI a halin yanzu.