A ranar 31 ga watan Agusta na shekarar 2023, aka gudanar da bikin kafa ofishin sakataren tsarin mu’amala tsakanin ƙawacen jami’o’in Sin da Afirka da kwamintin nazarin ilmin Sin da ƙungiyar haɗin gwiwar jami’o’in Afirka suka shirya tare.
Shugaban kwamintin nazarin ilmin koyarwa a jami’o’in Sin Du Yubo da mataimakinsa Zhang Daliang, da sakataren kwamintin jami’o’in Afirka Olusola Oyewole, da sakataren kwamitin jami’ar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua da mataimakinsa kuma shugaban Yang Dan, da mataimakin sakataren janar kwamitin nazarin koyarwa a jami’o’i Hao Qingjie sun sanar da buɗe ofishi a hukunce.
A ƙarƙashin shugabancin ma’aikatar kula da ilmi da kwamintin nazarin ilmi a jami’o’i, ofishin sakatare na ɓangaren Sin zai gudanar da ayyukan mu’amala da haɗin gwiwa da sauran hukumomin nazarin Afirka tare, don kafa tsarin haɗin gwiwa a hukunce.