A ranar 4 ga watan Satumba, an ƙaddamar da bikin bude sabon zangon karatu ga sabbin ɗaliban shekarar 2023 na jami’ar BFSU. Sabbin ɗalibai 3267 za su shiga jami’ar, don buɗe wani sabon shafi ga rayuwarsu.
Sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU da mataimakinsa kuma shugaban BFSU Yang Dan, da abokin karatu a shekarar 1973 kuma tsohon mataimakin shugaban sashen kula da tuntuɓawar ƙasashen waje na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminisancin ƙasar Sin Ai Ping sun halarci bikin.
Yang Dan ya yi jawabi mai take don zama fitacce ɗan jami’ar BFSU mai kishin ƙasa, da son nazari, don maraba da taya murna ga sabbin ɗalibai. Sakataren Wang ya miƙa katin jami’ar gare su. Sabbin ɗalibai sun sa bajin jami’ar don zama ɗan BFSU a hukunce.