A zagayowar shekaru 10 da aka gabatar da manufar Ziri Ɗaya da Hanya Ɗaya, a ranar 16 ga watan Satumba, an ce, an shirya taron ƙoli kan wayewar kai ta duniya da BFSU ta shirya a BFSU. Taken taron shi ne “Ƙara mu’amala tsakanin wayewar kai ta duniya, da sa ƙaimi ga fahimtar juna”, wanda aka yi kira da a inganta mu’amalar wayewar kai, da tashi tsaye don shiga cikin aikin raya wayewar kai ta duniya, da hobbasa wajen kafa gamayyar ɗan Adam. Ƙwararru da masana da suka fito daga sassan daban daban da wakilan jami’o’in gida da waje, da wakilan malamai da ɗaliban BFSU sama da 600 sun halarci taron.
Babban sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya yi jawabi mai take “Ɗauki alhaki da ke wuya don raya wayewar kai ta duniya”. Mataimakin shugaban sashen dake kula da tuntuɓawar ƙasashen waje na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminisancin ƙasar Sin Guo Yezhou, da mataimakin shugaban bankin ICBC Zhang Weiwu, da tsohuwar babbar jami’ar hukumar UNESCO Irina Bokova, da shugaban jami’ar SJP ta Sri Lanka Pathmalal M. Manage sun yi jawabi bi da bi.
An fidda sakamakon nazarin al’adu da ilmi na ƙasashen da ke Ziri Ɗaya da Hanya Ɗaya, kuma ana fata gudanar da dandalin ba da hidima a hukunce, da bayar da adadin fahimtar ƙasashen duniya, don bayyana yadda BFSU ta dauka nauyin da ke wuyanta wajen nazari.
Mataimakin sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU kuma shugaban jami’ar Yang Dan ya yi muhimmin jawabi mai take “Sa kaimi ga inganta mu’amalar wayewar kai don ƙara fahimtar juna. Shugaban kwamitin kula da sada zumunta tsakanin Aljeriya da Sin Smail Debeche, shugaban zartaswa na jami’ar CMRU ta Thailand, Chatree Maneekosol, da shugaban kwamitin nazarin al’adun Confucius kuma Furfesa Roger T.Ames sun gabatar da jawabi ɗaya bayan ɗaya.
A gun tarurrukan tattaunawa da aka shirya, an mai da hankali a kan “Kalubale da makoma, haɗin gwiwa don fuskanta tare” da “Harshe da wayewar kai ta duniya” da “Yada labaru ta duniya da ƙara fahimta tsakanin bambancin al’adu”, da sauransu, kwararru da masana mahalartar taron sun yi mu’amala game da batuttukan da ke shafar wannan.