A ranar 27 ga wata, ministan kula da zirga-zirga da kafofin yada labaru kuma kakakin majalisar ministocin ƙasar Sri Lanka Bandula Gunawardana ya ziyarci BFSU. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jami’iyyar kwaminisancin jami’ar Yang Dan, da mataimakinsa Jia Wenjian sun gana da shi. Bangarorin biyu sun yi mu’amala game da inganta mu’amala da ƙarfafa haɗin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu game da horar da ɗalibai masu koyon Sinhalese da gudanar da aikin gwaji a ƙasashen waje.