A ranar 17 ga wata, shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Yang Dan ya gana da takwaransa na jami’ar KazNU Tuimebayev Zhanseit Kanseituly, wanda ya raka shugaban ƙasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev ziyarar ƙasar Sin don halartar taron ƙoli na ƙasa da ƙasa karo na uku kan Ziri Ɗaya da Hanya Ɗaya da aka yi a ƙasar Sin. Bangarorin biyu sun daddale yarjejeniya game da musayar ɗalibai a ƙarƙashin shaidawar shugaban CITIC na Sin Zhu Hexin.