A ranar 17 ga wata, sakataren ma’aikatar kula da gine-gine da sufuri na ƙasar Cambodiya kuma mataimakin shugaban kwamitin sada zumunci tsakanin ƙasashen Cambodiya da Sin H.E. Mr. Lau Vann ya ziyarci BFSU. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Yang Dan ya gana da su, inda suka musanyar ra’ayoyi game da mu’amalar al’adu da horar da ɗalibai a tsakaninsu.