A ranar 23 ga watan Oktoba, babbar jami’ar hukumar kula da ilmi da kimiyya da al’adu ta M.D.D UNESCO kuma shugabar kwalejin nazarin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa ta BFSU Irina Bokova ta gabatar da jawabi mai take al’adu da daidaita batutuwan duniya. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Yang Dan ya halarci bikin, kuma mataimakinsa Zhao Gang ya shugabanci shi.
Bokowa ta bayyana alaƙar dake tsakanin al’adu da samun ɗauwamammen ci gaba mai dorewa, kuma ta gabatar da matakai 17 na samun ci gaba mai dorewa da za a iya aiwatar da su, kuma sun tattauna da ɗalibai game da jinsi da samun ɗauwamammen ci gaba da ƙa’idojin duniya da yarjejeniyoyin duniya, da mayar da abubuwan gado da aka gada daga kaka da kakanni zuwa gida.
Bayan da aka bayar da jawabi, Bokova ta aika da littafin salon magana game da al’adu da tunanin ƙasar Sin na Sinanci da Turanci gare ta.