Babban Shafi > Labaru > 正文

Wang Dinghua ya shugabanci tawaga don ziyartar Argentina da Brazil da Costa Rica

Updated: 2023-11-23

Daga ranar 9 zuwa ranar 17 ga watan Nuwamba, babban sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya shugabanci tawaga don kai ziyara a ƙasashen Argentina da Brazil da Costa Rica, inda ya ziyarci jami’ar Belgrano, da jami’ar Buenos Aires ta Argentina, da jami’ar UNILA, da jami’ar Rua Marquês de São Vicente ta Brazil, da jami’ar UNED ta Costa Rica da sauran jami’o’i, inda aka daddale yarjejeniyoyin haɗin gwiwa, da nazarin sabbin hanyoyin haɗin gwiwa game da ilmi, da nazari, don fadada haɗin gwiwa a wajen koyarwa a Intanet da samar da gwajin ayyukan yi, da sabon tunanin kafa kwalejin Connfucius da haɗin gwiwa tare. A yayin ziyara, sun ziyarci ƙaramin ofishin jakadancin Sin dake Rio da ofishin jakadancin Sin da ke Brazil da Costa Rica, inda suka yi mu’amala da mambobin ofishin jakadancin Sin da ke wurin da abokan karatu. A yayin ziyara, Farfesa Wang ya tattauna batun watsa shirye-shirye da harsuna da dama na gidan talebijin dake shafar ilmi na ƙasar Sin, kana sun gana da malamai da ɗaliban BFSU dake gudanar da nazari a shekarar 2023.