A ranar 24 ga watan Nuwamba, an shirya taron tattaunawar Shanghai kan nazarin ƙasar Sin a duniya. Taken taron da aka yi shi ne wayewar kan al’ummar Sin da hanyoyin da aka bi a ƙarƙashin yanayin duniya da ake ciki. Shugaban BFSU kuma mataimakin zaunannen kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Yang Dan ya shugabanci tawaga don halartar taron.
Yang Dan ya gabatar da jawabi a yayin taron tattaunawar koyi da juna a tsakanin wayewar kai ta duniya: kwatata wayewar kan al’ummar Sin ta zamani, ya yi jawabi mai take manyan tsare-tsare game da harsuna, a yi amfani da harshe don sa ƙaimi ga mu’amala da koyi da juna tsakanin ƙasashen duniya.
Ofishin yada labarun majalisar gudanarwar Sin kuma gwamnatin Shanghai sun shirya taron tare, inda aka bayar da kafa haɗaɗɗen kwamitin nazari kan ƙasar Sin, tare da bayar da gudummawar musamman game da sha’anin nazarin ƙasar Sin na shekarar 2023. Ƙwararru da masana sama da 400 da suka fito daga ƙasashe da yankuna sama da 60 sun halarci taron.