Daga ranar 7 zuwa ranar 9 ga watan Disamban, an shirya taron ƙasa da ƙasa game da Sinanci na shekarar 2023. Taken taron shi ne“A yi amfani da Sinanci don ba da hidimomi ga duniya.” Ƙwararru da masana na gida da waje, da jami’an gwamnati, da wakilan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da shugabannin hukumomin harsunan ƙasashen duniya kimanin 2000 sun halarci taron. Sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua, da zaunannen mamban kwamitin kuma mataimakin shugaban BFSU Jia Dezhong da Jia Wenjian sun halarci taron, inda suka yi jawabin fatan alheri a tarurruka da dama, gami da shugabantar manyan tarurruka da yawa.