Babban Shafi > Labaru > 正文

Shugaban BFSU ya ziyarci ƙasashen Habasha, Madagascar, da Tanzaniya

Updated: 2023-12-20

Daga ranar 1 zuwa ranar 10 ga watan Disamban, shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren janar kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Yang Dan ya shugabanci tawaga don kai ziyara a ƙasashen Habasha, Madagascar, da Tanzaniya, inda suka ziyarci kamfanin CCECC a Habasha da jami’ar Addis Ababa da cibiyar yaƙi da cututtuka ta ƙungiyar AU, da ofishin mataimain firaministan ƙasar kuma ministan harkokin wajen ƙasar, da laburaren adanan kayayyakin tarihi da bayanan hukuma, da ofishin ilmin ƙungiyar AU, da kwalejin koyon ilmin malanta na Antananarivo na Madagascar da kwamitin Sinawa a ƙasar, da jami’ar Dar es Salaam ta Tanzaniya da cibiyar nazarin ƙasar Sin, da kwalejin Confucius, da kamfanin StarTimes a kasar, da kamfanin CCECC a yankin gabashin ƙasashen Afrika, da kamfanin CHEC da ke ƙasar Tanzaniya. BFSU ta fadada hanyar haɗin gwiwa da shahararrun jami’o’in Afrika, da kafa sabon nau’in horar da ƙwararru da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa don samar da guraben ayyukan gwaji. Ban da wannan kuma, sun ziyarci ofishin jakadancin Sin a ƙungiyar AU da ƙasashen Madagascar da Habasha da Tanzaniya, inda suka yi mu’amala da jami’an dake wurin.