A ranar 28 ga watan Febrairun shekarar 2024, BFSU ta fara share fagen ayyukan da za a gudanar da su a sabon zangon karatu.
Babban sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya fara jibge ayyuka a hukunce. Na farko, za a zage damtse don tantance karatun digiri na farko. Na biyu kuma, za a fara hangen nesa game da haɓaka fannonin karatu. Na uku kuma, za a inganta ingancin fitattun fannonin karatun BFSU. Na huɗu, za ƙarfafa aikin raya jam’iyyar kwaminisancin Sin da horar da ɗalibai tare. Na biyar, za a ilmantar da ɗalibai daga duk fannoni. Na shida, za a zaɓi fitattun jami’ai daga cikinsu. Na bakwai, za a kyautata albarkatun da ake da su. Na takwas, za a inganta ƙwarewar gudanar da ayyuka. Na tara, za a ƙarfafa mu’amala a cikin gida da waje. Na goma, ba za a yi ƙasa a yi gwiwa ba don samun ci gaba.
A fannin inganta mu’amala da haɗin gwiwa, sakataren Wang ya yi nuni da cewa, za a hoɓɓasa wajen buɗe ƙofa ga ƙasashen waje yayin da ake haɓaka sha’anin ilmi, za a shigar da fitar da ƙwararru don buɗe sabon babin inganta haɗin gwiwa da ƙasashen waje. Za a ƙoƙarta wajen inganta haɗin gwiwa da fitattun jami’o’i 200 da nagartattun jami’o’i a ƙasashen da ake koyar da harsunan da ba a nazari sosai a kan su ba. Za a ƙara kyautata ingancin ɗaliban da za a ɗauka, don ƙago sabon tsarin ɗalibta a jami’ar BFSU.