
Daga ranar 8 zuwa ranar 17 ga watan Afrilu, sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya shugabanci tawaga don ziyartar ƙasashen Nepal, da Vietnam, da Indonesiya, inda suka ziyarci jami’o’in Tribhuvan, da Kathmandu, da Nepal Sanskrit dake birnin Kathmandu na ƙasar Nepal, da jami’ar Hanoi dake nazarin doka, jami’ar nazarin cinikayyar ƙasashen waje, da jami’ar HUE dake nazarin dokokin ƙasar Vietnam, kuma sun ziyarci cibiyar raya harsunan ma’aikatar kula da harkokin ilmi a birnin Bandung, da jami’ar koyon ilmin Indonisiya da sauran hukumomin gwamnati, inda suka tattauna sabuwar hanyar raya haɗin gwiwa da fitattun jami’o’in dake nazarin harsuna da cinikayyar ƙasashen waje da dokoki da ilmi a ƙasashen kudancin Asiya da kudu maso gabashin Asiya, ta hakan za a raya haɗin gwiwa da su wajen nazarin ƙasashen duniya da shiyya-shiyya, da ƙago sabbin fannonin mu’amala a fannin koyarwa da nazari. Sakataren Wang ya ziyarci ofisoshin jakadancin Sin da ke ƙasashen Nepal da Vietnam da Indonisiya, da ƙaramin ofishin jakadancin Sin a birnin Ho Chi Minh, inda kuma ya gana da abokan karatu na jami’ar a ƙasashen waje da sauran kamfanoni, kuma sun kafa ƙungiyar abokan karatu na BFSU a ƙasar Indonesiya, wadda ta zama ta 11 a duniya.