A ranar 29 ga watan Afrilu, ministan kula da ilmi, da wasanni, da matasa, da nazari, da ƙirƙiro da sabbin tunani na Malta Clifton Grima ya ziyarci BFSU, inda ya gana da shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar da mataimakinsa Zhao Gang.
Grima ya gabatar da jawabi mai taken “Horar da ƙwararru daga dukkan fannoni”, inda ya amsa tambayoyin da aka yi game da tsarin ilmin jami’ar Malta, da horar da matasa, da ilmi da ƙirƙiro da sabbin tunani, da raya wasanni da sauransu.
Kafin aka yi jawabin, ɗaliban BFSU masu koyon harshen Malta sun rera waƙar harshen, inda suka samu yabo daga baƙi, kuma sun ziyarci ɗakunan nune-nunen harsunen duniya na BFSU.