A ranar 20 ga watan Mayu, ministan harkokin ilmin ƙasar Belarus Andrei I. Ivanets ya shugabanci tawaga don ziyartar BFSU. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Jia Wenjian da mataimakinsa Zhao Gang sun gana da shi, inda bangarorin biyu suka yi mu’amalar mutane da al’adu tsakaninsu. Babbar jami’ar ma’aikatar kula da harkokin ilmin ƙasar Sin Xi Ru ta halarci ganawar.
Bayan ganawar, ɗaliban kwalejin nazarin Rashanci na BFSU sun karanta rubutacciyar waƙar Belarus da nuna musu kiɗe-kiɗen gargajiya, gami da shaida musu nasarorin da suka samu a fannin koyon harshen Belarus da Rashanci. Ban da wannan kuma, tawagar ta ziyarci cibiyar nazarin Belarus ta BFSU, inda aka jinjina nasarorin da cibiyar ta samu, gami da yin mu’amala da malamai da ɗalibai.