A ranar 31 ga watan Mayu, an gudanar da shirin haɗin gwiwa tsakanin jami’o’in Sin da Afirka 100 a tsakaninsu a BFSU. Sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU kuma direktan shirin mu’amalar da tsakanin ƙawacen shirin mu’amalar jami’o’in Sin da Afirka 100 Wang Dinghua, da mataimakin shugaban kwamintin nazarin koyarwa a jami’o’in Sin, da sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar ZJNU kuma mataimakin direktan shirin haɗin gwiwa Jiang Yunliang sun yi jawabi. A nasa ɓangare, Sakataren kwamintin jami’o’in Afrika Olusola Bandele Oyewole ya yi jawabin fatan alheri ta hoton bidiyo. Wakilan mambobin ƙawacen jami’o’i sama da 150 sun halarci taron.
A yayin taron, jami’o’in Sin da suke ckin shirin haɗin gwiwa sun bayar da shirin gudanar da aiki. Wang Dinghua ya yi sharhi da cewa, dalilin da ya sa aka gudanar da shiri saboda horar da ƙwararru tsakanin Sin da Afrika, da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin shawarwari da aka yi tsakanin shugabannin Sin da Afrika a birnin Johannesburg. A watan Agustan shekarar 2023, BFSU ta karɓi baƙuncin gudanar da shirin mu’amala kuma ta zama mamban wannan shiri.