Daga ranar 14 zuwa ranar 15 ga wata, an gudanar da taro karo na 6 game da shirya darussa online na ƙawacen jami’o’in koyar da harsunan wajen Sin da ke da taken haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen duniya don samu makoma mai hashe kuma taro karo na uku na kwaikwayon ainihin koyarwa online a BFSU.
Shugaban ƙawacen jami’o’i kuma babban sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya gabatar da rahoto, kuma mataimakinsa na ƙawacen kuma shugaban BFSU Jia Wenjian ya shugabanci bikin ƙaddamar da taron.
Jami’in sashen kula da yada labaru na kwamintin tsakiya na jam’iyyar kwaminisancin Sin Long Tao da jami’in ma’aikatar kula da ilmin Sin Song Yi, da sauran wakilan jami’o’i a ƙawacen kuma mataimakin shugaban jami’ar Shan Dong Cao Xiaoqiang da mataimakin shugaban jami’ar GDUFS Jiao Fangtai sun yi jawabin fatan alheri bi da bi.
An gudanar da taron tattaunawar shugabannin jami’o’in ƙawace don lalubo bakin zaren ingiza sha’anin koyarwa a lokacin. An gudanar da bikin musayar darussa tsakanin ƙawacen jami’o’i da na ƙasar Thailand, don fara gudanar da aikin raya darrussa online na ƙawace.