A ranar 28 ga watan Yuni, an gudanar da bikin kammala karatu na shekarar 2024 na BFSU a hukunce. Ɗaliban da suka samu digiri na farko, da na biyu da na uku sama da 2800 sun halarci bikin.
Jakadan ƙasar Malaysia a ƙasar Sin Dato’ Norman Muhamad, abokin karatu na kwalejin nazarn dokokin BFSU kuma shugaban kamfanin kimiyya da fasaha na Beijing Baman Tianxia Zhang Tianyi Zhang Tianyi, da sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua da mataimakinsa kuma shugaban BFSU Jia Wenjian da sauran shugabanni sun halarci bikin. Shugaban Jia ya yi jawabin fatan alheri mai take “Rungumi dunya don ƙara samun bunkasuwa.” Yayin da Sakataren Wang ya miƙa iznin shaida abokan karatun BFSU, gami da miƙa tutar BFSU ga ɗaliban masu neman digirgiri karo na 26 da za su gudanar da aikin koyarwa sa kai a ƙasar.