A ranar 25 ga watan Yuli, an gudanar da taron tattaunawar jama’a karo na 7 kuma taron shugabannin matasa karo na 7 a birnin Changsha dake lardin Hunan. Shugabanni da tsoffin shugabanni da shugabannin matasa da na jam’iyyu na ƙasashen Afirka sama da 50 da wakilan ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba da ƙwararru da matasa kimanin 200 sun halarci taron. Shugaban jami’ar BFSU kuma mataimakin sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian, da zaunannen mamban kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Dezhong su ma sun halarci taron.
A gun bikin buɗe taro, an fidda sakamakon da aka yi shiri za a samu ta hanyar gudanar da shirin kyawawan abokan jama’ar Sin da Afirka na Hanyar Siliki Don Samun Fahimtar Juna, BFSU ta gabatar da shawarar kafa ƙawacen ba da hidimar masu aikin sa kai da shirin ilmin masu gudanar da aikin mata na Sin da Afirka, kuma sauran shirye-shirye da BFSU da kamfanin Alibaba da sauran hukumomi suka gabatar game da raya fasahar AI da sauransu.
A wannan rana da yamma, an gudanar da taron tattaunawar matasa masu aikin sa kai na ƙasa da ƙasa. BFSU ta gabatar da shawarar kafa asusun masu aikin sa kai na ƙasa da ƙasa na duniya. Asusun ya kasance wani babban sakamakon da ƙawacen masu aikin sa kai na duniya ya samu game da raya haɗin gwiwa da mu’amala a tsakanin ƙasashen Sin da Afirka. Mataimakin sakataren haɗaɗɗen kwamintin masu aikin sa kai na Sin Duan Guiqing da mataimakin sakataren kwamintin sa kaimi ga mu’amala a tsakanin ƙungiyoyin jama’a Wang Ke da shugaban BFSU Jia Wenjian sun sanar da kafa ƙawace da kafa wannan asusu a hukunce.