
A ranar 5 ga watan Satumba, an gudanar da taron shekara-shekara na tsarin mu’amalar ƙawacen jami’o’in Sin da Afirka a birnin Beijing. BFSU ta shirya wannan taro, taken taron shi ne haɗin gwiwa da samun bunƙasuwar ilmin jami’o’in tsakanin Sin da Afirka a sabon yanayin da ake ciki. Wakilan jami’o’i 35 na ƙasashen Afirka 19 ciki har da Tanzaniya, da Nijeriya, da Afirka ta Kudu, da Kenya, da Habasha, da Tunisiya, da Ghana, da Uganda, da Rwanda, da Kamaru, da Malawi da Benin da Kongo(Kinshasa), da Mozambique, da Somaliya da sauran jami’o’in Sin kimanin 50 sun halarci taron.
Bayan da aka kammala bikin buɗe taron, an gudanar da bikin rattaba hannu kan manyan ayyukan haɗin gwiwa game da ilmi a tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Afirka da sakamakon haɗin gwiwa da aka samu. An sa hannu game da haɗin gwiwar ilmi tsakanin Sin da Afirka 14 a nan, kuma an gudanar da dandalin haɗin gwiwa na tsarin mu’amalar ƙawace a hukunce. Sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminisancin ƙasar Sin kuma direkta mai zartaswa na ƙawace Wang Dinghua da takwaransa na ƙasashen Afirka Olusola Oyewole kuma sakataren kwamintin jami’o’in Afirka sun gabatar da rahoto game da tsarin ɗaya bayan ɗaya.
An gudanar da shawarwari guda uku a yayin taron. Shugabannin jami’o’in Sin da Afirka sun yi mu’amala sosai game da haɗin gwiwa da more ilmi a ƙarƙasin yanayin da ake ciki, da ilmi da mu’amala ta ƙetaren bambancin al’adu, da haɗin gwiwar Sin da Afirka da horar da ɗalibai.