JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Mambar dake kula da harkokin ƙirƙire-ƙirƙire da nazari da al’adu da ilmi da matasan kwamitin EU ta ziyarci BFSU

发布时间:2024-04-12

A ranar 30 ga watan Maris, mambar da ke kula da harkokin ƙirƙire-ƙirƙire da nazari da al’adu da ilmi da matasan kwamitin EU da take halartar tsarin mu’amalar al’adu da jama’a karo na 6 tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Turai Iliana Ivanova ta ziyarci BFSU. Mamban kwamitin jam’iyyar kwaminisancin ma’aikatar kula da ilmin Sin Chen Jie da direktan kula da haɗin gwiwa da mu’amala da ƙasashen waje na ma’aikatar da babban sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua sun halarci bikin, mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar BFSU kuma mataimakin jami’ar Jia Wenjian ya shugabanci taron.

A yayin bikin, mataimakin ministan Chen Jie ya miƙa wa Iliana Ivanova da ragowar baƙi littattafan da BFSU ta tsara. Wang Dinghua da Ivanova sun yi jawabin fatan alheri.

A yayin kammala bikin, Ivanova ta ziyarci sashen koyon harshen Bulgarian, kuma ta tambayi halin da ake ciki wajen koyar da sauran harsunan ƙungiyar EU. Daga bisani kuma, tawagar ta ziyarci lambun sada zumunta tsakanin ƙasashen Sin da Turai.NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC