JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Takaitaccen bayani kan jami’ar BFSU


Jamiar koyon harsunan waje ta Beijing tana arewa da zoben hanya ta uku a yankin Haidian da ke birnin Beijing, kuma an kafa sashi na gabas da na yamma a gefuna biyu na hanyar, kuma jamiar tana karkashin shugabancin maaikatar kula da ilmi ta kasar Sin, kuma tana daya daga cikin jamioi dari da Sin za ta kokarta bunkasuwa tun daga  karni na 21, kuma tana daya daga cikin jamioin da ke da kyawawan fannoni masu fiffiko a cikin shirin raya kyawawan jamioin da Sin ta gabatar a watan Mayu na shekarar 1998, kana kuma tana daya daga cikin fitattun jamioin da Sin take bunkasuwa yanzu.

Jamiar BFSU ita ce jamiar koyon harsunan waje ta farko da jamiyyar kwaminis ta Sin ta kafa, kuma da ma, ita ce, sashin kungiyar koyon Rashanci na uku na jamiar koyon ilmin soji da siyasa don yaki da milkin mallaka na Japan ta kasar Sin, wadda aka kafa a shekarar 1941, sannan kuma an bunkasa ta har ta zama makarantar koyon harsunan waje ta Yanan, kuma lokacin da aka kafa ta, tana karkashin shugabancin kwamitin tsakiya na jamiyyar kwaminis ta kasar Sin. Bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin, maaikatar kula da harkokin waje ta fara shugabantar makarantar, a shekarar 1954, an canja sunanta zuwa kwalejin koyon harsunan waje na Beijing, a shekarar 1959 ne, aka hada ta da kwalejin koyon Rashanci na Beijing don ya zama sabon kwalejin koyon harsunan waje na Beijing. Bayan shekarar 1980, maaikatar kula da ilmi ta Sin ta fara shugabantarta kai tsaye, a shekarar 1994, an canja sunanta zuwa jamiar koyon harsunan wajen Sin.

An amince da BFSU da ta bude harsunan waje 101, inda kungiyar harsunan Turai da ta Asiya da ta Afrika sun kasance sansanonin nazarin harsunan da ba safai da aka yi amfani da su mafi girma a kasar Sin, kuma sun kasance fannonin karatu na musamman da maaikatar ilmi ta amince da su karo na farko. Yanzu, a hannu daya, BFSU ta kokarta raya fannonin karatu na koyon harsunan waje da adabinsu, a hannu dayan kuma, aka daidaita bunkasuwar sauran fannoni kamar adabi da dokoki, da tattalin arziki da harkokin gudanar da ayyuka da sauransu. Tun daga farko zuwa yanzu, an fara bude Rashanci, Turanci, Faransanci, Jamusanci, da harshen Spain, da na Poland, da na Czech, da harshen Romaniya, da Japananci, Larabci, da harshen Cambodiya, da na Laos, da harshen Sinhalese, da harshen Malaysiya, da na Sweden, da na Portugal, da na Hungary, da na Albaniya, da na Bulgariya, da harshen Swahili da na Burma, da harshen Indonesiya, da na Italiya, da na Croatiya, da na Serbiya, da harshen Hausa, da na Viemnam, da harshen Thailand, da na Turkiya da na Koriya, da na Slovakiya, da na Finland, da na Ukraine, da na Holland, da na Norway, da na Iceland, da na Danmark, da na Girka, da na Philippines da harshen Hindu, da Urdu, da Hebrew, da Persian, da harshen Sloveniya, da na Estoniya, da na Latviya da na Lithuaniya da harshen Irish, da na Malta da na Bangladesh, da harshen Kazak da Uzbek, Latin, Zulu, da Kyrgyz da Pushutu, da Sanskrit, da Pali da Amharic, da Nepal, da Somali, da Tamil, da Turkmen, da Catala da Yoruba, da harshen Mongoliya, da na Armeniya, da Malagasy, da harshen Georgia, da na Azerbaijan, da Afrikaans, da Macedonian da Tajik, da Setswana da Ndebele da Comorian, da Creole, da Shona, da Tigrinya, da Belarusian, da Maori, da Tangan, da Samoan, da Kurdish, da Bislama, da Dari, da Tetum, da Dhivehi, da Fijian, da Cook Islands Maori, da Kirundi, da Luxembourgish, da Kinyarwanda, da Niuean, da Tok Pisin, da Chewa, da Sesotho, da Sango, da Tamazight, da Javanese, da kuma Punjabi

Yanzu, akwai sassan koyarwa da nazari 33 a jamia, a cikin yan shekarun nan, jamiar BFSU ta kafa kwalejin nazarin kasa da kasa da jamiar Nottingham ta Birtaniya, kuma bi da bi ne, ta kafa kwalejin nazarin harsuna na Xu Guozhang da kwalejin nazarin adabin kasar waje na Wang Zuoliang, da kwalejin nazarin daidaita batutuwan shiyya-shiyya da na duniya, da kwalejin nazarin mu’amalar al’adu da kwatanta wayewar kai, da sauran hukumomin nazari da ke da halayyen musamman. BFSU tana karfafa tsarin yin gyare-gyare game da horar da dalibai, kuma ta kafa kwalejin BFSU, da kwalejin nazarin kungiyoyin kasa da kasa, da kwalejin nazarin ilmin kasa da kasa. A karkashin tsohon kwalejin nazarin nahiyar Asiya da ta Afrika, an kafa kwalejin nazarin Asiya, da kwalejin nazarin Afrika. Yanzu, jami’ar tana da muhimman sansanonin nazarin ilmin mutane da al’adu da zamantakewar al’umma na ma’aikatar ilmi ta kasar Sin, kamar cibiyar nazarin harsunan waje da koyarwa ta kasar Sin, da cibiyar nazarin harsunan kasar, da cibiyar nazari da raya harsunan kasar. Kana tana da sansanoni 4 na horaswa da nazarin shiyya-shiyya da kasashe na ma’aikatar harkokin ilmin Sin, wato cibiyar nazarin yankin tsakiya da gabashin Turai, da cibiyar nazarin Japan, da cibiyar nazarin Ingila, da cibiyar nazarin Canada, da ma ragowar cibiyoyi 37 na nazarin shiyya-shiyya da kasashe da maaikatar kula da ilmi ta amince da su. Haka kuma, tana da cibiyoyi 3 na nazarin musayar mutane da aladu na maaikatar kula da ilmi ta kasar wato cibiyar nazarin musayar aladu da mutane tsakanin kasashen Sin da Indonesiya, da cibiyar nazarin musanyar aladu da mutane tsakanin Sin da Faransa, da cibiyar nazarin musayar aladu da ke tsakanin Sin da Jamus. Dadin dadawa kuma, jamiar ta buga mujalloli guda 4 na CSSCI wato mujallar nazari da koyar da harsunan kasashen waje, da mujallar nazarin adabin kasashen waje, da mujallar dandalin kasashen duniya, da mujjalar nazarin Sinanci a kasashen waje, kuma tana da mujallar nazarin ilmin da ke kan gaba game da koyar da harsunan waje, wadda ta kasance daya daga cikin mujallolin da za su zama na CSSCI. Haka kuma, ta buga mujallar koyar da Rashanci a Sin, da mujallar ilmin nazarin harsuna don muamala na Sin da harshen Turanci, da mujallar ilmin koyar da Sinanci a duniya, da mujallar koyon Turanci, da mujallar nazarin mutane da al’adu ta Jamus, da mujallar nazarin kasashe da shiyya-shiyya dake amfani da harshen Faransanci, da mujallar nazarin bunkasuwar shiyya-shiyya da duniya. Haka kuma, jami’ar tana da sansanin buga littatafai da fitar da faifan bidiyo da na’urorin harsunan waje mafi girma a kasar Sin, wato kamfanin kula da harkokin buga littatafan dake shafar koyarwa da nazarin harsunan waje.

[ 1 2 ]

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC