JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Laburare

LABURARE

2019年04月16日


Fadin laburaren jami’ar BFSU ya kai murabba’in mita dubu 23, akwai hawaye guda 6, ya zama ginin musamman cikin jami’ar, a bangon kofar laburaren, an rubuta rubuce-rubuce da harsuna 55, abun da ya nuna al’adu na musamman da yanayin kasashen duniya na jami’ar, a cikin ginin, akwai wani madubin dake da rubuce-rubuce, idan akwai hasken rana, tamkar ana cikin kogin ilmi. A tsakiyar dakin Laburaren, akwai wani tsani da ya yi kama da wani tsauni ne, don nuna al’adun kasar Sin na hawan dutsen ilmi. Duk fasalin da aka yi, ya nuna halayyen musamman na laburaren, kuma an tanada littatafai a ciki, kuma akan iya aron littatafai a ciki, abun da ya nuna tunanin raya laburare na zamani.

Akwai littatafai iri na takardu na gida da waje da yawansu ya kai miliyan 1.264, kana akwai littatafan gida da waje a shafunan yanar gizo da yawansu ya kai dubu 482, kana akwai mujallun gida da waje dubu 1.174 da wurin adana bayanan gida da waje 56, kuma, an samu littatafai da bayanan dake shafar harsuna da tarbiya, da al’adu. A cikin ‘yan shekarun nan, bayan da jami’ar BFSU ta kara bunkasa, an kafa tsarin adana littatafan dake shafar dokoki, diplomasiyya, tattalin arziki, yada labaru, tafiyar da harkokin ciniki da sauransu.

Laburaren ya samar da kujeru kimanin 2000 ga masu karatu da dakunan nazari 18, kana an kafa dakin gabatar da bayanai da dakin nazari, da ajin horarwa, da dai sauransu. A sa’i daya kuma, an bayar da dakin nune-nune, da dakin shayi da sauran dakunan nishadantarwa. Ba ma kawai, ana iya samun ilmi a laburare, kana akan iya yin mu’amala da kara-wa-juna-sani, duk wadannan sun nuna tunanin fasalin laburare na BFSU na dora muhimmanci game da kawo moriya ga jama’a.Ban da wannan kuma, an bude harkokin mayar da littafai baya cikin awoyi 24 ga laburare, kuma akan iya gurzawa da dab’in da aron da mayar da littatafai da kanka. Dakin karatu ya adana nau’rorin zamani, ba ma kawai zai iya bayar da yanayin karatu ga masu karatu ba, kana zai iya sa kaimi ga masu karatu su kirkiro da sabon tunani. Dakin karatu ya yi amfani da hanyoyin zamani don tafiyar da harkoki,ba ma kawai ya nuna halin zamani na dakin karatu, kana ya nuna yanayin zamani na gaggauta raya tattalin arziki da ilmi.

Labararen BFSU ya samar da dimbin littatafai da ni’imtattun yanayin karatu da kyawawan hidimomin zamani ga masu karatu, kuma ya zama wurin karatu da na nazari har ma da na mu’amala mai kyau ga dalibai da malamai a jami’ar.
NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC