JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Mujaloli

2019年04月15日


中国法律与文化年度课程

A ranar 21 ga watan Satumba, ma’aikatar kula da ilmi da ma’aikatar kula da harkokin kudi da kwamitin kula da gyare-gyare da raya kasa na Sin sun fidda sanarwar jerin sunayen jami’o’in da kyawawan fannonin karatu da kasar Sin za ta kokarta don raya su, ta yadda za a habaka su har sun zama na gaba-gaba dai a duniya. A cikin sanarwar, jami’ar BFSU ta shiga cikinsu, kuma gwamnatin Sin za ta hobbasa don raya fannonin karatun jami’ar.

A cikin jerin sunayen jami’o’in Sin da kasar za ta kokarta don raya su, an hada da kyawawan jami’o’i 42, da jami’o’in wadanda suke da fitattun fannonin karatu 95, BFSU ta kasance daya daga cikinsu.

全球外语大学联盟配图

A ranar 19 ga watan Mayu, an yi taron tattaunawa kan nazarin shiyya-shiyya da daidaita lamuran duniya kuma taron tattaunawa tsakanin kawacen jami’o’in harsunan waje na duniya. Jami’ar BFSU ta shirya kafa wannan kawace, kuma jami’o’i 30 na kasashe 16 na duniya sun zama mambobin farko a cikin wannan kawacen. Mataimakin ministan harkokin ilmin Sin Tian Xuejun da babban sakataren jami’ar BFSU Han Zhen da shugaban jami’ar Peng Long sun halarci taron.

An kafa wannan kawace bisa irin halayyen musamman na jami’o’i wajen nazarin shiyya-shiyya da kasashe daban daban, kuma wannan kawace zai bi akidar hadin gwiwa da amincewar juna, da samun moriyar juna tare, don kafa wani dandalin hadin gwiwa kan ilmi, bisa karfin nazarin harsunan waje da koyar da su, da nazarin shiyya-shiyya da kasashen daban daban, don inganta mu’amalar jama’a tsakaninsu.

An kafa kwamitin kawacen kuma shugaban jami’ar BFSU Peng Long zai zama shugaban kawacen, sauran shugaban jami’o’i za su zama mambobin kwamitin, kuma an kafa ofishin sakatariyar kwamitin a BFSU. Za a yi wani taron tattaunawa a ko wadannan shekaru biyu-biyu, don tattauna batun tunanin inganta jami’o’i, da hanyar samun bunkasuwa da horar da kwararru, da inganta fannin karatu da dai sauransu, don tabbatar da ayyukan hadin gwiwa da daddale yarjejeniyoyi.

A yayin taron, wakilan mambobin kawacen, sun daddale yarjejeniyar hadin gwiwa, don shaida kafa wannan kawace a hukunce.

Mambobin kawacen jami’o’in harsunan waje na duniya sun hada da jami’ar harsunan Azerbaijan, da jami’ar Sofia ta Bulgariya, da jami’ar Lima ta Peru, da kwalejin nazarin harsunan waje na biyu na Beijing, da jami’ar koyon harsunan waje ta Beijing, da jami’ar nazarin harsuna ta Beijing, da kwalejin nazarin tafinta na Munich,da jami’ar koyon harsunan waje ta Dalian, da jami’ar koyon harsunan waje ta Tokyo, da jami’ar koyon ilmin tattalin arziki da cinikin kasashen waje ta Sin, da jami’ar koyon ilmin harsunan waje da cinikayya ta Guangzhou, da kwalejin nazarin dangantakar kasa da kasa na Sin, da jami’ar Al Farabi ta kasar Kazakhstan, da jami’ar koyon harsunan waje ta Koriya ta Kudu, da kwalejin nazarin dangantakar kasa da kasa na Moscow, da jami’ar koyon harsunan waje ta Moscow, da jami’ar kasar Mexico da jami’ar Muhammed ta Morocco ta biyar, da jami’ar koyon ilmin tattalin arziki da cinikin kasashen waje ta Shanghai, da jami’ar koyon harsunan waje ta Shanghai, da jami’ar koyon harsunan waje ta Sichuan, da jami’ar koyon harsunan waje ta Tianjin, da kwalejin nazarin ilmin diplomasiyya na Sin, da jami’ar nazarin harsunan kasashen duniya ta Uzbekistan,da jami’ar koyon harsuna ta Kivu ta kasar Ukraine, da jami’ar koyon harsunan waje ta Xian, da jami’ar Gujarat ta tsakiya ta kasar India, da jami’ar Yogyakartata kasar Indonesiya, da kwalejin koyon harsunan waje na Zhejiang, da jami’ar Católica de Valparaíso ta Chile.

彭龙校长会见(修改尺寸后)

A ranar 17 ga watan Febrairu, shugaban jami’ar BFSU Peng Long ya gana da takwaransa na jami’ar Reading ta Birtaniya David Bell da direktan cibiyar nazarin kimiyya da sadarwar kasuwancin Henry Furfesa Liu Kecheng, inda bangarorin biyu suka tattauna hadin gwiwa tsakaninsu.

Shugaban Peng ya yi maraba da Bell da ya sake ziyarar jami’ar BFSU bayan shekara ta 2013, kuma ya yi farin ciki da ganin hadin gwiwar jami’o’in biyu cikin shekaru da dama da suka gabata, kuma yana fatan jami’o’in biyu za su ci gaba da karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu. Bayan da Bell ya ji bayani game da bunkasuwar BFSU, ya ce, yana sa ran jami’o’i biyu za su karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu. Bangarorin biyu sun tattauna dalla-dalla game da musayar dalibai da horar da masu neman digiri na uku cikin hadin gwiwa, da yin hadin gwiwa tsakanin kwalejin kasuwanci na jami’o’i biyu a tsakaninsu. Shugaban kwalejin nazarin kasuwanci na kasa da kasa Niu Huayong wanda ya halarci taron.

MUJALOLI


Mujaloli Da Akan Buga A Kowane Lokaci

Nazari Da Koyar Da Harsunan Waje(Muhimman)

Adabin Kasashen Waje (Muhimman)

Dandalin Duniya (Muhimman)

Koyar Da Rashanci A Sin

Koyon Turanci

Koyon Faransanci

Koyon Rashanci

Nazarin Al’adun Jamusanci

Sinanci A Kasashen Duniya

Koyar Da Sinanci A Kasashen Duniya (Sinanci/Turanci)NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC