JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

BFSU ta fara share fagen sabon zangon karatu na 2024

发布时间:2024-03-04

A ranar 28 ga watan Febrairun shekarar 2024, BFSU ta fara share fagen ayyukan da za a gudanar da su a sabon zangon karatu.

Babban sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya fara jibge ayyuka a hukunce. Na farko, za a zage damtse don tantance karatun digiri na farko. Na biyu kuma, za a fara hangen nesa game da haɓaka fannonin karatu. Na uku kuma, za a inganta ingancin fitattun fannonin karatun BFSU. Na huɗu, za ƙarfafa aikin raya jam’iyyar kwaminisancin Sin da horar da ɗalibai tare. Na biyar, za a ilmantar da ɗalibai daga duk fannoni. Na shida, za a zaɓi fitattun jami’ai daga cikinsu. Na bakwai, za a kyautata albarkatun da ake da su. Na takwas, za a inganta ƙwarewar gudanar da ayyuka. Na tara, za a ƙarfafa mu’amala a cikin gida da waje. Na goma, ba za a yi ƙasa a yi gwiwa ba don samun ci gaba.

A fannin inganta mu’amala da haɗin gwiwa, sakataren Wang ya yi nuni da cewa, za a hoɓɓasa wajen buɗe ƙofa ga ƙasashen waje yayin da ake haɓaka sha’anin ilmi, za a shigar da fitar da ƙwararru don buɗe sabon babin inganta haɗin gwiwa da ƙasashen waje. Za a ƙoƙarta wajen inganta haɗin gwiwa da fitattun jami’o’i 200 da nagartattun jami’o’i a ƙasashen da ake koyar da harsunan da ba a nazari sosai a kan su ba. Za a ƙara kyautata ingancin ɗaliban da za a ɗauka, don ƙago sabon tsarin ɗalibta a jami’ar BFSU.NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC