JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

BFSU ta shirya bikin tura ɗalibai ƙasashen waje don gudanar da bincike a lokacin hutu a hukunce

发布时间:2023-07-19

A ranar 30 ga watan Yuni, BFSU ta shirya bikin tura ɗalibai ƙasashen waje don gudanar da gwajin aiki da bincike a hukunce a shekarar 2023. Manyan baƙi da suka fito daga ma’aikatar ilmin Sin, da hukumar ladabtarwa ta kwamitin tsakiya, da kamfanin gine-gine da shimfida layin dogo, da kamfanin zirga-zirgar Sin, da kamfanin Fuhua, da bankin Sin, da kamfanin Alibaba, da kamfanin JD, da kamfanin dillancin labaru na Xinhua, da kamfanin jaridar China Daily, da tashar Internet ta Renmin sun halarci bikin.

Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar ya yi jawabi mai take ‘Sauke nauyin dake wuya don nuna yanayin da ƙasar Sin ke ciki’. Shugaban tawagar fahimtar shawarar ‘Ziri Ɗaya da Hanya Ɗaya’ ta Jamus Wang Jianbin, da malamin da ke jagorancin tawagar nazarin fasaha da al’adu na ƙananan kabilu na ƙasashen da ke ‘Ziri Ɗaya da Hanya Ɗaya’ Ning Qiang, da mamban tawagar bincike na shiga kurmin Birch Ling Fu, da mamban tawagar Caravan Shen Yishu sun yi jawabi bi da bi.

Shugaban Yang ya sanar da ƙaddamar da tawagogin bincike a hukunce, kuma ya danka tutoci ga tawagogi 43 na BFSU.

Wannan karo na farko da jami’o’in Sin suka ƙaddamar da tawagogin bincike a lokacin hutu, wanda ke ƙarƙashin shugabancin malamai da aka bayar ga ɗaliban BFSU a hukunce. A shekarar 2023, jami’ar za ta tura tawagogi 43 dake ƙunshe da malamai da ɗalibai sama da 500 don gudanar da bincike a nahiyoyin biyar na duniya.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC