JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Shugaban BFSU ya ziyarci Faransa da Birtaniya da Swiss

发布时间:2023-06-27

Daga ranar 6 zuwa ranar 15 ga wata, shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Yang Dan ya shugabanci tawaga don ziyartar ƙasashen Faransa, Birtaniya, da Swiss, inda suka ziyarci kwalejin nazarin al’adu da harsuna na INACO, da kwalejin kasuwanci na Turai, da jami’ar siyasa ta Paris, da jami’ar OU ta Birtaniya, da kwalejin nazarin tattalin arziki da siyasa na London LSE, da jami’ar Brookes Oxford, da kwalejin nazarin kasuwancin HSBC na jami’ar Peking a sashen Oxford, da jami’ar London, da kwalejin nazarin Asiya da Afirka ta jami’ar SOAS, da kwalejin nazarin samun bunƙasuwa da raya dangantakar ƙasa da ƙasa ta Geneve a Swiss, da ƙungiyar raya ilmi, da kimiyya da al’adu na M.D.D. da ofishin Geneva na M.D.D watau UNESCO, da cibiyar nazari da horaswa ta M.D.D, da hukumar koyarwa ta ƙasa da ƙasa ta UNESCO, da ƙungiyar raya hakkin kare ilmin duniya, da ƙungiyar ba da agaji ta Red Cross, don lalubo bakin zaren inganta haɗin gwiwa da jami’o’in da suka yi fici wajen harsuna, da kimiyya, da siyasa, da tattalin arziki, ta yadda za a tattauna salon horar da ɗaliban ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa , da ƙara samar da guraben ayyukan gwaji, da ƙirƙiro da sabbin tunani wajen raya kwalejin Confucius na sassa a ƙasashen waje, kana mambobin tawagar sun ziyarci ofisoshin jakadancin Sin da ke ƙasashen Faransa, UNESCO, da Birtaniya, don yin mu’amala da jami’o’in diflomasiyya, kuma jami’o’i sun gana da abokan karatu da ɗalibai, da shugaban kwalejin Confucius da malamai, da masu aikin sa kai da aka tura a waɗannan ƙasashe.



NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC