A ranar 6 ga watan Yuni, shugaban jam’iyyar zamantakewar al’umma da demokuradiyya ta Jamus Lars Klingbeil ya shugabanci tawaga don ziyartar BFSU, inda ya yi jawabi. Sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua, da mataimakinsa Jia Wenjian sun gana da shi. Kllingbeil ya yi jawabi mai take “Zaman doka da oda a sauyin yanayin da ake ciki”, inda ya amsa tambayoyin da ɗalibai da malamai suka bayar gare shi.