Daga ranar 20 zuwa ranar 30 ga watan Mayu, sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya shugabanci tawaga don ziyartar ƙasashen Belgium, da Hungary da Spaniya, inda ya ziyarci kwamitin Belgium da Sin, da kwalejin Confucius na Brussel, kana ya halarci kwas ɗin na Sinanci na kwalejin Confucius don yalwata haɗin gwiwa a sabbin fannoni, kuma ya ziyarci jami’ar Liège da kwalejin Confucius na jami’ar, inda aka daddale yarjejeniyar musayar ɗalibai, kazalika ya ziyarci sashen tafinta na ƙungiyar EU don tattauna aikin haɗin guiwa da kwalejin nazarin fasara na BFSU. A yayin ziyararsa a Hungary, ya ziyarci jami’ar Eotvos Lorand, da tattauna haɗin gwiwa da kwalejin Confucius na jami’a, inda aka kafa dangantakar abokantaka da daddale yarjejeniyar haɗin gwiwa da musayar ɗalibai, kuma ya halarci bikin cika shekaru 100 da kafa kwalejin nazarin Sinanci na jami’ar, da ci gaba da tattauna haɗin gwiwa da su. Haka kuma, ya ziyarci kwalejin kimiyya na Hungary don tattauna haɗin gwiwa da su. A yayin ziyararsa a Spaniya, ya ziyarci jami’ar Barcelona, da kwalejin Confucius a wuri, don tattauna haɗin gwiwar shiyya-shiyya da su. Haka kuma, a yayin ziyarar, ya ziyarci ofisoshin jakadancin Sin da ke ƙasashen Belgium, da Hungary, da Spaniya, kuma ya yi taron tattaunawa da jami’an diflomasiyya na waɗannan ƙasashe da ƙungiyar EU, kuma ya gaida shugaban kwalejin Sinanci da malamai da masu aikin sa kai a waɗannan ƙasashe.