A ranar 12 ga watan Janairu, kwalejin kula da tantance nazarin kimiyyar zamantakewa da al’adun ƙasar Sin ta bayar da rahoto game da tantance mujallolin nazarin kimiyyar zamantakewa da al’adu na ƙasar na AMI na shekarar 2022, inda aka bayar da sakamakon da suka samu. Mujallolin BFSU sun yi fice a cikin wannan aikin tantance na wannan karo, mujalla ɗaya ta zama fitacciyar mujalla, yayin da sauran mujalloli 5 sun zama kyawawan mujalloli, kuma mujalloli 3 sun shiga cikin jerin kyawawan mujalloli, kuma sauran mujalloli 25 sun shiga cikin tsari.
Kwalejin kula da tantance nazarin kimiyyar zamantakewa da al’adun ƙasar Sin ta shirya wannan aiki, kuma ya bayar da wannan rahto a ko waɗanne shekaru huɗu-huɗu. Rahoton tantance mujalloli na AMI ya yi tasiri sosai a hukumomin nazarin ƙasar Sin.