Kwanan baya, an kammala ayyukan nazari da suka shafi al’adu da ilmi na ƙasashen da ke hanyar Ziri Ɗaya da Hanya Ɗaya, watau ayyukan nazarin al’adu da ilmi na ƙasashen India, Iran, Cuba, Keya. Gaba ɗaya ne, aka kammala rubuta ayyukan nazari 20 da suka ƙunshe da taƙaitaccen bayani, da al’adu, da ilmi, da tarihi, da tarbiya, da ilmin makarantar firamare, da na midil, da makarantar horar da malamai, da manufar ilmi, da yanayin da ake ciki game da mu’amala da sha’anin ilmi da ƙasar Sin a ƙasashen Albaniya, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Habasha, Angola, Congo(Brazawille), North Macedonia, Mongoliya, Morocco, Mozambique, Senegal, Nepal, Tanzaniya, Tajikistan, Singapore, Hindu, Ukraine, da Jordan da sauran ƙasashe 20. Waɗannan ayyuka sun ƙara sanin masu karatu game da ilmi da al’adu na ƙasashen, kuma abun da ya bayar da shawara, da sabon tunani game da sha’anin yin gyare-gyare da samun bunƙasuwa game da tsarin ilmi a ƙasar Sin.