JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An gudanar da taron ƙara-wa-juna-sani da fitar da mujallar Confucius ta duniya a BFSU

发布时间:2022-09-02

A ranar 26 ga watan Agusta, an gudanar da taron ƙara-wa-juna-sani da fitar da mujallar Confucius ta duniya da harshen Turanci da kwamintin haɗin gwiwa kan nazarin Confucius na duniya, da jami’ar BFSU suka shirya tare, kuma kamfanin kula da ɗab’in littattafan koyar da harsunan waje da nazari ya ɗauki nauyin shiryawa. Shugabar kwamintin nazarin Confucius na duniya Liu Yandong ta yi jawabin fatan alheri.

Mataimakin shugaban kwamintin nazarin Confucius na duniya Chen Lai da sauran mambobin kwamintin Wang Niannig, da Zhang Xuezhi, da Li Yan, da Wang Xuedian, da An Leizhe, da sakataren janar na kwamintin Jia Deyong, da babban editan mujallar kuma shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Yang Dan, da jami’in kula da ɗab’in koyarwa na ma’aikatar kula da ilmi ta Sin Chen Rui, da shugabar kamfanin ɗab’in Wang Fang sun halarci taron. Mataimakin shugaban BFSU kuma mamban zaunannen kwamintin jam’iyyar kwaminis ta jami’ar BFSU Zhao Gang ya shugabanci taron.

Mujallar Confucius ta duniya ta zama wata babbar mujalla, wadda ta ingiza mu’amalar wayewar kai, da ƙirƙiro da sabbin tunani, da nuna abubuwan nazari, da kafa gadar sada zumunta. A watan Mayu na shekarar 2021, kwamintin ya fitar da mujalla da harshen Sinanci. A wannan karo, an fitar da mujallar da harshen Turanci, wanda zai ci gaba da inganta yalwata ra’ayin Confucius da al’adun gargajiya na ƙasar Sindon sanya tunanin Sin ga warware batuttuwan duniya, da kafa wani dandanlin ƙirƙiro da sabbin tunani da mu’amala tsakanin masu nazarin Confucius na duniya.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC