JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An karramawa masu aikin sa kai na BFSU

发布时间:2022-04-22

A ranar 19 ga wata, kwamitin gasar wasannin Olympics na Beijing da kwamitin gasar wasannin Olympics ta naƙasassu ta Beijing sun shirya bikin karramawa a Beijing.

Tawagar masu aikin sa kai na BFSU da cibiyar ba da taimako ta wayar tarho da harsuna daban daban na gasar wasannin Olympics ta Beijing da gasar wasannin naƙasassu ta Beijing sun samu lambar yabo ta fitattun ƙungiyoyi a gasar wasannin Olympics da gasar wasannin Olympics ta naƙasassu ta Beijing, mai aikin sa kai Liu Zhipeng da Ye Wenxiaoyu sun samu lambobin yabo na fitattun masu aikin sa kai. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren jam’iyyar kwaminisancin BFSU Yan Dan ya halarci taron, kuma wakilan masu aikin sa kai 20 su ma sun halarci taro.

A yayin gasar wasannin Olympics da gasar wasannin Olympics ta naƙasassu ta Beijing. BFSU ta aika da masu aikin sa kai 900 don ba da hidimomi ga ɗakunan filaye 10 na Beijing da Zhang Jiakou, da wuraren miƙa lambobin yabo, da cibiyar wasannin Olympics da cibiyar yaɗa labaru da otel-otel da sauransu. BFSU ta zama jami’ar da ta tura masu aikin sa kai mafi yawa, inda suka ba da taimako a ɗakunan filaye mafi yawa. Ban da wannan kuma, a matsayin babbar cibiyar da BFSU ta ɗauki nauyin shiryawa, cibiyar ba da taimako da harsuna daban daban ta waya, ta ba da taimakon fassara ga tawagogin daban daban a lokacin wasanni.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC