JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An ƙaddamar da taron ƙolin tattaunawar gyare-gyare da bunƙasuwar sha’anin koyar da harsunan waje a jami’o’in ƙasar Sin

发布时间:2022-04-09


Daga ranar 19 zuwa ranar 20 ga watan Maris, aka ƙaddamar da taron ƙoli karo na 6 na tattaunawar gyare-gyare da bunƙasuwar sha’anin koyar da harsunan waje a jami’o’in ƙasar Sin. Taken taron shi ne ƙara fahimtar ƙasar Sin da tuntuɓawar ƙasashen waje.

Mataimakin shugaban hukumar kula da yaɗa labaru na ƙasa da ƙasa na sashen kula da yaɗa labaru na kwamintin tsakiya na ƙasar Sin Chen Xueliang da mataimakin direktan dake kula da jami’o’in ƙasar Sin Wu Shixing da tsohon jakadan Sin a ƙasar Birtaniya Zha Peixin da babban sakataren jam’iyyar kwaminisancin ƙasar Sin Wang Dinghua sun yi jawabi game da koyar da ɗalibai masu aikin fassara da tafinta don ƙara cudanyar Sin da ƙasashen duniya, da ƙarfafa aikin gyare-gyare game da fannonin karatun fasaha, don horar da ɗalibai masu koyon harsuna na zamani, da sauke nauyin dake wuyansu wajen ba da gudummawa, da kyautata matsayin jami’o’in Sin wajen tinkarar ƙalubalen duniya.

Babban sakatare Wang Dinghua ya gabatar da matakai 10 da za a ɗauka don haɓaka jami’o’in Sin wajen tinkarar ƙalubalen duniya, watau a tantance yadda za a koyar da ɗalibai masu idanun duniya, da masu halayyen duniya, da ƙara horar da jami’o’in ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da ƙara haɓakar jami’o’in Sin a ƙasashen waje, da shigar da fitattun fasahohin koyarwa na duniya, da bayyana tunanin tinkarar ƙalubalen duniya, da raya sha’anin nazarin batutuwan duniya, da tashi tsaye don tsara ƙa’idojin duniya, da samar da taimakon koyarwa a ƙasashen duniya, da ƙara yalwata mu’amalar al’adu da tarbiya tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen waje.

An kafa tarurruka guda 9, ƙwararru da masana 92 sun tattauna sabon yanayin da ake ciki wajen koyar da harsunan waje na zamani da sabon ci gaba da aka samu.

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC