JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Beijing ta cika alkawarin da ta ɗauka na shirya wasannin Olympics ba tare da gurɓata muhalli ba

发布时间:2022-02-10

A ranar 9 ga watan Fabrairu, bisa labarin da jaridar Economic Daily ta Sin ta bayar, an ce, a yayin taron manema labarun da kwamitin gasar wasannin Olympics na duniya da kwamitin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing suka shirya, shugaban kula da tsare-tsaren kwamitin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing Li Sen ya taƙaita nasarorin da gasar wasannin Olympics ta samu, inda ya bayyana cewa, kiyaye muhalli ya zama wani muhimmin ci gaban da aka samu.

Gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta yi amfani da ɗakuna 6 na gasar wasannin Olympics ta shekarar 2008. A sa’i ɗaya kuma, birnin Zhang Jiakou ya yi amfani da makamashi masu kiyaye muhalli, inda ya samar da wutar lantarki ga wuraren wasanni 3 na Beijing da Yanqing da Zhang Jiakou, kuma an cimma burin samar da wutar lantarki ba tare da gurɓata muhalli ba. A cikin shekaru 6 da suka gabata, an cimma burin rage hayaƙi mai gurɓata muhalli, don tabbatar da cimma burin shirya gasar wasanni ba tare da gurɓata muhalli ba.

Yankin Yanqing ya kasance wani wurin wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing, inda ke da albarkatun muhalli. An ɗauki matakai da dama don farfado da muhallin halittu a wurin.

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC