JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Gu Ailing: Zan gabatar da wasan gudu a kan dusar ƙanƙara ga matasan Sin

发布时间:2022-02-08

Bisa labarin da kafofin yada labarun ƙasar Sin CNS ya bayar, an ce, an gudanar da gasar samun izinin shiga gasar ƙarshe ta wasan gudu a kan dusar ƙanƙara cikin ’yanci ta mata ta hanyar tsalle daga dandalin gasar Olympics a lokacin sanyi ta 2022, inda ’yar wasan ƙasar Sin Gu Ailing ta halarci gasar.

Bisa labarin da aka samu, an ce, tun daga shekarar 2019, Gu Ailing ta fara shiga gasa a matsayin wata ’yar wasan ƙasar Sin. Haka kuma tana fatan za ta gabatar da wannan wasa ga matasan Sin, da kuma dukkanin ma’abotan wannan wasa. Ba ta amince da cewa dole ne sai an girma sosai, sannan za a haifar da tasiri ga duk duniya ba. Tana ganin cewa, lokaci ya yi da ya kamata a yi canje-canje, watau matasa su tofa albarkacin bakinsu game da batutuwan da suka shafi kansu.

A halin da ake ciki yanzu, yawan mutanen Sin da suka shiga wasannin dusar ƙanƙara da wasannin ƙanƙara ya kai miliyan 300. Gu Ailing ta ce, tana son yalwata wasan gudu a kan dusar ƙanƙara, don morewa farin ciki da ƙaunar da take samu. Ko da yake yunkurinta bai taka kara ya karya ba, amma tana fatan kwalliya za ta biya kuɗin sabulu.

Yayin da ake zantawa da ita game da yadda take ganin shiga gasar Olympics a karo na farko a ƙasar Sin, ta nuna zane-zanen da ke rigarta, ta zayyana wannan da kanta, wadda zanen rigar ke ɗauke da al’adun ƙasar Sin.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC