JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Nesa ta zo kusa

发布时间:2022-02-08

Bisa labarin da shafin Internet na Tianshan na ƙasar Sin ya bayar, an ce, a yammacin shekaranjiya 5 ga watan Fabarairu, Dinigeer Yilamujiang da abokiyar wasanninta a ƙungiyar ƙasar Sin Bayani Jialin suka fara wasannin gudu a kan dusar ƙanƙara na ƙetaren daji na gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing. Haka kuma, wannan shi ne karo na farko da aka samu ’yan wasan daga birnin Altay dake jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta ƙasar Sin a tarihin gasar Olympics ta lokacin sanyi, inda aka laƙaba wa birnin sunan “Asalin wasan gudu a kan dusar ƙanƙara”.

A daren ranar 4 ga wata, Dinigeer ta zama ɗaya daga cikin manyan masu yaɗa tocilan wasanin Olympics, ta tsaya a dandalin wasanni mafi ƙoli na duniya, abun da ya cika burin mahaifinta Yilamujiang Miraj. Ya nuna farin ciki sosai game da wannan, sabo da shi ma ya taɓa zama ɗan wasan gudu a kan dusar ƙanƙara, har ya rasa abun da zai ce, ganin nesa ta zo kusa. Dinigeer, ’yar kabilar Uyghur ce, wadda aka haifa a birnin Altay da ke jihar Xinjiang a yankin arewa maso yammacin ƙasar Sin. Ta fara wannan wasa tare da mahaifinta ne tun tana da shekaru 8 a duniya.

Dalilin da ya sa ake kiran birnin a matsayin “Asali wasannin gudu a kan dusar ƙanƙara” shi ne, a wani kogon Dunde Brak da ke birnin, akwai wani zane mai launuka daban daban da aka yi a kan duwatsu, inda aka aka nuna yadda kaka da kakanni suka taka kan katako, ɗauke da sanda don safarar dabbobi. Bisa nazarin da masana suka yi, an ce, wannan zane ya daɗe har shekaru sama da dubu 120, kuma ya zama abun gado mafi yawan shekaru da aka fi sani, wanda ya shaida cewa mutane sun yi wasan gudu a kan dusar ƙanƙara.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC