JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An kaddamar da bikin tura matasa masu aikin sa kai na BFSU zuwa wasannin Olympics na lokacin sanyi na 2022 na Beijing

发布时间:2022-01-20

   

A ranar 18 ga watan Janairu,an kaddamar da bikin tura matasa masu aikin sa kai na BFSU zuwa gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing da gasar wasannin Olympics ta nakasassu. Haka kuma, wannan biki ya kasance bikin fara ba da hidimomi da harsunan daban daban na Beijing a hukunce. Mataimakin shugaban kula da sashen tuntubawar waje na kwamintin shirya wasannin Olympics na Beijing Wan Xuejun da babban sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin BFSU Wang Dinghua, da mataimakin sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminis kuma shugaban jami’ar Yang Dan, da mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminis Su Dapeng, da zaunannen mamban kwamintin jam’iyyar kwaminis kuma mataimakin shugaban jami’ar Ding Hao sun halarci bikin.

A yayin bikin wasannin Olympics, BFSU za ta tura masu aikin sa kai sama da 900 don ba da hidimomi ga wasannin. A madadin jami’ar, babban sakataren jami’ar Wang Dinghua ya mika tuta ga masu aikin sa kai na jami’ar, abun da ya alamanta cewa, an fara gudanar da aikin ba da aikin sa kai a hukunce.

A lokacin wasannin Olympics, cibiyar ba da taimako da harsuna daban-daban ta Beijing, za ta ba da hidimomin fasara da harsuna 21 ga wasannin Olympics. Mista Yang Dan da Wan Xuejun da malamai da dalibai masu aikin sa kai sun sanar da ba da hidimomi a hukunce.

Wan Xuejun ya jinjina malamai da dalibai da suka ba da hidimomi a wasannin Olympics, inda ya jaddada cewa, dole ne su sauye nauyin da ke wuyansu da yin amfani da fiffikonsu don ba da hidimomi a wasannin Olympics. Yayin da Su Dapeng ya nanata cewa, kamata ya yi malamai da dalibai su gaji tunanin masu aikin sa kai, da gudanar da aiki yadda ya kamata. Kana ya kamata su kokarta don gabatar da Sin ga duk duniya. A madadin jami’ar, Ding Hao ya mika kayayyaki ga masu aikin sa kai.

A nasu bangare kuma, wakilin malamai masu aikin sa kai Guan Bo, da wakiliyar masu aikin sa kai Ye Wenxiaoyu, da wakilin iyayen masu aikin sa kai sun gabatar da jawabi bi da bi.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC