JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

BFSU ta samu damar gudanar da manyan ayyukan nazari 5 da asusun kula da nazarin kimiyyar zamantakewar al’umma zai ba da kyautar kudi

发布时间:2021-12-28

Kwanan baya, an fidda takardar sunayen manyan ayyukan bincike dake shafar kimiyyar zamantakewar al’umma na shekarar 2021. An amince da manyan ayyuka 4 da BFSU ta gabatar, wanda ya dau matsayi na 21 a kasar Sin. A sa’i daya kuma, rukunin kula da asusun nazarin kimiyyar zamantakewar al’ummar Sin ya amince da cewa, BFSU dake karkashin shugabancin farfesa Wang Dinghua, babban sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar za ta dauki matsayin tsara littattafan koyarwa na harsunan waje game da fahimtar kasar Sin ta zamani, kuma an nada wannan aikin nazari a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan nazari da asusun kimiyyar zamantakewar al’umma zai kebe kudin musamman don gudanar da su a shekarar 2021.

Tuni, BFSU ta samu damar gudanar da ayyukan nazari 16 da asusun kula da kimiyyar zamantakewar al’umma za ta kebe kudaden musamman don gudanar da su, da ayyukan nazarin kimiyyar halittu guda 5, da ayyukan nazarin al’adun mutane da ma’aikatar ilmi za ta kebe kudaden musamman don gudanar da su, da ayyukan nazari guda 5 da birnin Beijing za ta kebe kudaden musamman don nazari. Wadannan ayyukan nazari sun shafi fannonin karat una harsuna, da adabi, da yada labaru da tafiyar da harkoki, da nazarin batutuwan kasa da kasa.



NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC